Kasar Rasha ta yi Allah wadai da hare-haren ta’addancin da ake kai wa a Siriya.
Kakakin fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya bayyana harin ta’addanci a matsayin ” keta ‘yancin kasar Siriya.”
Ya bayyana fatan cewa Damascus za ta shawo kan lamarin cikin gaggawa.
A ranar Laraba ne mayakan takfiriyya karkashin jagorancin Hayat Tahrir al-Sham suka kaddamar da wani gagarumin hari a lardin Aleppo da Idlib da ke arewa maso yammacin kasar, inda suka kwace yankuna da dama.
A ranar Juma’ar da ta gabata ce tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta harshen Larabci ta bayar da rahoton cewa, sojojin kasar Siriya sun kaddamar da wani farmaki na mayar da martani.
A cewar al-Mayadeen, ana ci gaba da gwabza kazamin fada a yammacin Aleppo.
An kuma dakile wasu manyan hare-hare guda hudu da aka kaddamar daga birnin Anadan da ke arewacin Aleppo.
Kafin hakan Jiragen yakin Rasha da na Siriya sun yi ruwan bama-bamai a yankunan da ‘yan ta’adda suka mamaye a arewa maso yammacin Siriya kusa da kan iyaka da Turkiyya.
Tun a shekara ta 2011 ne dai kasar ta Syria ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke samun goyon bayan kasashen waje inda Damascus ke zargin kasashen yammacin duniya da kawayen su na yankin da taimakawa kungiyoyin ‘yan ta’adda.