Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bakin mai Magana da yawunta Maria Zakharova tayi gargadin cewa martani da kasar rasha za ta mayar kan harin da jirage marasa matukin Ukrain suka kai kan gidan shugaban kasar viladmir putin ba zai zama martani na diplomasiya ba,
Kakakin ta fadi cewa a ranar litinin bayan da ministan harkokin wajen rasha Sergey Lavrov ya sanar a daren ranakun 28-29 ga watan decemba Kasar Ukrani ta kaddamar da hari mai cin dogon zango kan gidan shugaban kasar viladmir putin sai dai an kakkabe harin babu wani rahoto game da jikkata ko lalata wuri,
Kakakin ta kara da cewa harin na Ukrain kamar mari ne a fuskar turmph , adaidai lokacin da kasar rasha ta dage tana tattaunawar zaman lafiya da kasar Amurka ta shiga tsakani lavrov ya bayyana cewa zaa sake tunani kan matsayin tattaunawar saboda matakin da kasar Ukrain ta dauka, ya tabbatar da cewa an gano wuraren da zaa kai hare-haren ramuwar gayya.
Sai dai shugaban kasar Ukrain Volodmyr Zelenske ya musanta kai harin, yace farfaganda ne kawai kasar rasha ta kitsa,domin ta lalata ci gaban da ake samu a alakar da ke tsakaninta da kasar Amurka, ya zargi kasar rasha da kokarin neman mafaka yadda za ta kai mata hari