Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa a daren jiya Alhamis ta kakkabo da jiragen sama marasa matuki na kasar Ukireniya 121 bayan sun shiga cikin sararin samaniyar kasar.
A wani bayani da ya fito daga ma’aikatar tsaron kasar ta Rasha ta ci gaba da cewa;An dakatar da kokarin da Ukireniya ta yi a daren jiya na yin kutse a cikin sararin samaniyar kasar Rasha da kai hare-haren ta’addanci.
Haka nan kuma sanarwar ta ce, an kakkabo 6 daga cikin jiragen sama marasa matukin an kakkabo su ne a samaniyar yankin Rasha, sai kuma wasu 6 a samaniyar yankin Bilgorard. Har ila yau, Rashan ta kakkabo wasu jiragen sama marasa matuki 3 a samarn yankin Forvinge da kuma wasu 2 a yankin Tola.
Sauraun yankunan da aka kakkabo jiragen sama marasa matukin sun kunshi Oriyol, da Libistic a kuma da jamhuriyar Cremia.
Wannan hare-haren dai na Ukiraniya akan Rasha suna faruwa ne a daidai lokacin da Amerika take maganar kokarin kawo karshen dake tsakanin kasashen biyu.
Shugaban Amruka Donald Trump wanda ya gana da shugaban kasar Ukiraniya ya ce, ya bayyana masa amincewa da shirin tabbatar da zaman lafiya, domin kawo karshen yaki da Rasha.