Search
Close this search box.

Rasha Ta Gargadi Kasashen Dake Shirin Bai Wa Ukraine Makamai

Kasar Rasha ta sake gargadin kasashen dake kokarin bai wa Ukarine makamai. Rasha ta yi wannan gargadin ne a daidai lokacin da ta karbi shugabancin

Kasar Rasha ta sake gargadin kasashen dake kokarin bai wa Ukarine makamai.

Rasha ta yi wannan gargadin ne a daidai lokacin da ta karbi shugabancin kwamitin tsaro na MDD na wannan watan Yuli.

Vassily Nebenzya, wakilin Rasha a MDD, ya bayyana gataron taron ‘yan jarida cewa : duk wani mataki na bai wa Ukraine makamai ba zai haifar da ‘da mai ido ba, sannan kuma zai fuskanci mayar da martini na siyasa inji shi.

Kuma a cewar a kwana da sanin cewa za’a lalata dukkan makamman, kamar yadda aka lalata na kasashen yamma da Amurka.

Jakadan na Rasha a MDD, ya kuma tabo batutuwa da dama inda ya bukaci a kawo sauye-sauye a kwamitin tsaro na MDD, saboda rashin adalci da ake nunawa musamman ga Afrika, wacce ba ta da wakilci sosai a kwamitin sulhu idan akayi la’akari da kasashen yammacin duniya da sukayi kane-kane a kwamitin.

Vassily Nebenzya,  ya bayyyan ajandar kwamitin tsaron MDD na wannan watan Yuli, inda za’a gudanar da manyan taruka guda uku game da huldar kasa da kasa a bias tsari na cin moriyar juna da adalci a ranar 16 ga wata, sai kuma wata muhawara a game da warware rikici a Gabas ta Tsakiya wacce ministan harkokin wajen kasar Sergueï Lavrov, zai jagoranta a ranar 17 ga watan Yuli.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments