Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta bada sanarwan cewa sojojin kasar sun kakkabo jiragen yakin na kasar Ukrain har guda 31 a dare guda.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar ma’aikatar fadar haka. Ta kuma kara da cewa a daren Lahadin da ta gabata ce na’urorin garkuwan sararin samaniyar kasar Rasha suka kakkabo jiragen yakin.
Labarin ya kara da cewa jiragen yakin na kasar Ukraine nau’in wadanda ake sarrafasu daga nesa ne. Kuma an kakkabosu ne da yankuna daban daban na kasar, wato daga yankunan Biryans da Kaluga da begrad da Kurisk da Riyazan da Uryul da kuma Jumhuriyar Tataristan na kasar Rasha.
Labarin ya kara da cewa an kakkabo 14 daga cikinsu, kan lardin Biryansk sannan 6 a Kaluga sai 3 a bilgros sai kuma wasu 3 a yankin Kurask.