A yau Talata ne fadar mulkin Rasha ta “ Kremlin” ta sanar da cewa; Wasu daga cikin shugabannin kasashen yamma suna kokarin kunna wutar yaki a Ukiraniya, bayan da Kiev ta nemi zama cikakkiyar memba a cikin kungiyar Nato.”
Wannan tsokacin na Rasha dai ya zo ne a daidai lokacin da kungiyar kawancen yarjejeniyar tsaro ta Nato take gudanar da taro a matakin ministocin harkokin wajenta a birnin Brussels da can ne babbar cibiyar tarayyar turai.
Kakakakin fadar Kremlin Dmitry Pescov ya fada wa manema labaru cewa; Yiyuwar bai wa Ukiraniya damar zama memba, ba abu ne da Rasha za ta lamunta da shi ba, saboda barazana ce a gare ta.
Kasar Ukiraniya dai ta yi amfani da wannan taron na kasashen Nato, domin sake gabatar da bukatarta na ganin ta zama cikakkiyar memba a cikin kungiyar.
Rasha ta ce bai wa Ukiraniya damar zama memba a cikin wannan kungiyar da take dauka a matsayin abokiyar gaba, yana a matsayin baraza ce kai tsaye gare ta.
Pescov ya kuma ce wasu daga cikin kasashen turai suna son tsokanar Rasha ta hanyar kunna wutar yaki.