Kasar Rasha na wani babban taronta da abokan huldarta na Afirka a kasar Masar da nufin inganta dangantakar tattalin arziki da fadada tasirinta a Afirka.
Taron na zuwa ne a daidai lokacin da kawayen Ukraine ke kokarin maida Rasha saniyar ware ta fuskar diflomasiyya.
A karon farko dai, ana gudanar da wannan taron a nahiyar Afirka.
A cikin jawabinsa, ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya jaddada bukatar kiyaye hurumin nahiyar Afirka .
” A cewarsa, “mulkin mallaka na Yamma ya lalata tarihi na al’ummomin Afirka” kuma “mulkin mallaka na zamani ya ci gaba har zuwa yau.
” Rasha ta bayyana shirinta na yin aiki “tare da abokan hulɗarta na Afirka don kawar da waɗannan ayyuka.
” Ministan ya yi maraba da yadda Afirka ke ƙara samun shahara a fagen duniya, yana mai nuni da “farkawa ta biyu ta nahiyar” wadda abokan hulɗa ke goyon baya waɗanda ke girmama muradunta.
Moscow ta gabatar da kanta a matsayin ƙawa, wadda ta kuduri aniyar tsayawa tare da ƙasashen Afirka don ƙarfafa ikon mallakarta, tsaro, da ci gaba a dukkan fannoni: tattalin arziki, fasaha, abinci, makamashi, dijital, da kuma bayanai.
Ministan ya kuma yi maraba da ci gaban ciniki tsakanin Rasha da nahiyar Afirka, wanda ya kai dala biliyan 28 a shekarar 2024, wanda ya karu da kashi 13% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.