Rasha: Duniya Ba  Za Ta  Lamunta Da Yi Wa Kasashe Barazana Ba

Shugaban majalisar dokokin kasar Rasha “Duma” ya yi suka da kakkausar murya akan yadda wasu kasashen suka mayar da yi wa sauran kasashen duniya barazana

Shugaban majalisar dokokin kasar Rasha “Duma” ya yi suka da kakkausar murya akan yadda wasu kasashen suka mayar da yi wa sauran kasashen duniya barazana aikin dake gabansu.

Shugaban majalisar ta Duma ya ce; A cikin wannan duniyar wacce kasashe da dama suke da tasiri, ba zai zama karbabben lamari ba, a rika nunawa sauran kasashen duniya yatsa.

Shugaban majalisar kasar ta Rasha Vyacheslav Viktorovich Volodin wanda yake Magana akan zagayowar cikar babban zauren majalisar dinkin duniya shekar 80 da fara yin zama, ya rubuta cewa: An tsara ka’idoji da dokoki a duniya bayan kawo karshen yakin duniya na biyu domin tabbatar da sulhu da zaman lafiya da kuma kare hakkin dan’adam.

Volodin wanda bai ambaci sunan wata kasa ba, ya kuma ce; Sai dai a wannan lokacin, lamurra sun sauya da akwai  wasu kasashe da suke take dokokin kasa da kasa. An wayi gari suna yi wa wasu kasashen baraza da Shata musu wa’adin su aikata wani  abu da suke so,idan kuma aka amince da hakan, to rayuwar bil’adama ta gaba tana fuskantar hatsari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted