Rasha: Dawo Da Tsarin Takunkumai A Kan Iran Ya Saba Wa Dokar MDD

Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzya, ya ce maido da tsarin takunkuman karya tattalin arziki a kan Iran da wasu kasashen yammacin

Jakadan kasar Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vasily Nebenzya, ya ce maido da tsarin takunkuman karya tattalin arziki a kan Iran da wasu kasashen yammacin duniya suka yi ya saba wa kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya.

Nebenzya ya bayyana hakan ne a wata doguwar wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugaban rikon kwarya na kwamitin sulhun bayan da kasashe 15 suka kada kuri’ar sake kakaba takunkumi kan Tehran, wanda aka soke a karkashin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekara ta 2015 tsakanin Iran da manyan kasashen duniya, ciki har da Birtaniya, Faransa, da Jamus.

Wakilin na Rasha ya jaddada cewa, an bullo da abin da ake kira tsarin  dawo da takunkumai a kan Iran,  duk kuwa da kokarin diflomasiyya mai karfi da aka yi a makonni biyu da suka gabata, da kuma shirye-shiryen da Iran ta yi na neman mafita, saboda kasashen ukun sun yi watsi da duk wata matsaya da aka cimmawa tare da su.

Daftarin kudurin da shugaban majalisar ya gabatar a ranar 19 ga watan Satumba bai cika sharuddan kudurin 2231 ba, kuma sakamakon la’akari da hakan bisa doka ba za a iya maido da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya kan Iran ba, amma duk da hakan wasu mambobi na kwamitin sun yi watsi da hakan.

Jami’in diflomasiyyar na Rasha ya ce tun da kwamitin sulhun bai amince da wani kuduri kan tsawaita  kuduri mai lamba 2231 na MDD ba, to zai daina aiki daidai da ranar da aka cimma yarjejeniyar JCPOA a ranar 18 ga Oktoba, 2025.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted