Kasar Rasha ta sanar da samun nasarar gwajin jirgi maras matuki na nukiliya wanda yake ninkaya a cikin ruwa.
Gwajin dai ya biyo bayan wasu gwaje-gwajen da Rashan ta yi ne na makamai masu linzami samfura mabanbanta masu iya daukar makaman Nukiliya.
Jirgin maras matuki mai daukar makamin Nukiliya yana a karkashin rundunar sojan ruwan kasar,da aka bai wa sunan; Bosidon. Bugu da kari shi kanshi jirgin yana aiki ne da nukiliya a matsayin makamanshin da yake tafiyar da shi.
Shugaban kasar Rasha Vladmir ya ce; babu wata na’ura wacce za ta iya dakatar da wannan jirgin mai ninkaya a cikin ruwa na Nukiliya.
Shugaban kasar ta Rasha ya kara da cewa; Wannan sabon makamin babu kwatankwacinsa a duniya saboda saurinsa da kuma nisan inda zai iya isa.
A gefe daya shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bai wa sojojin kasar umarnin sake bude gwaje-gwajen makaman Nukiliya.
Shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya rubuta a shafinsa na “Truth Social” cewa, ya bayar da umarnin sake dawo da gwaje-gwajen makaman Nukiliya.