Search
Close this search box.

Rasha : Amurka Ce Ke Da Alhakin Harin Uklraine A Sevastopol

Rasha ta ce Amurka ce ke da alhakin harin makami mai linzamin da Ukraine ta harba wanda ya kashe fararen hula ciki har da kananan

Rasha ta ce Amurka ce ke da alhakin harin makami mai linzamin da Ukraine ta harba wanda ya kashe fararen hula ciki har da kananan yara a yankin Crimea.

Hukumomin Rasha sun ce wasu mutum fiye da dari sun jikkata, bayan makamin ya fada a gefen teku, inda mutane ke shakatawa a kusa da Sevastopol.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce an kai harin ne da makami mai linzami kirar ATACMS, wanda Amurka ta kera, kuma ta yi ikirarin cewa kwararru daga Amurkan ne suka tsara yadda za a kai harin.

Rasha ta ce ta harbo hudu daga cikin makaman masu linzamin da aka kai mata harin da su.

A cewar ma’aikatar lafiya ta kasar Rasha mutane 124 da suka hada da kananan yara 27 ne suka jikkata yayin da wasu mutane 3 da suka hada da kananan yara biyu suka mutu a harin da sojojin Ukraine suka kai masu da makami mai linzami na Amurka a yankin Sevastopol.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments