Rasha: Alummar Iran Tana Da Hadin kai Da Kishin Kare Kasar 

kasar rasha ta bayyana iran a matsayin alumma mai hadin kai da kishin kare kasa

Mataimakin shugaban majalisar tsaron kasar Rasha Dmitry Medvedev ya bayyana cewa ya samu alummar iran kan su a hade kuma suna da kishi da kudurin kare kasarsu daga duk wata barazana daga ko ina,

Jami’in na kasar rasha yayi wannan bayani ne a wata hira da yayi da gidan talabijin din kasar iran a jiya Asabar, medvadev ya bayyana yanayin yadda babban birnin tehran ya kasance a lokacin janaizar jagoran juyin musulunci na  iran  Ayatullah Sayyed Ali khamnei, yanayi ne mai cike da hadin kai tsakanin alummr kasar

Medevade da ya taba zama shugaban kasar Rasha a shekara ta 2008 zuwa shekara ta 2012 ya bayyana a lokacin hirata su cewa ziyarar tasa tazo ne kai tsaye bisa umarnin shugaban kasar rasha Vladmir Putin na halartar jana’izar da kuma girmama shahid Ayatullah Khamana’I, saboda putin yana daukarsa da wani matsayi na musamman don haka ya bukaci na halarci jana izar

Haka zalika ya kara da cewa duk da wahalhalun da ake ciki na lokacin yaki da kuma ci gaba da kai hare haren Amurka amma yanayin rayuwa tana gudana kamar yadda aka saba a birnin Tehran, wata gaskiya ce da ya bayyanata da zata amfani duk wani mai sa ido,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted