Ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar da cewa kasar a shirye take ta taimaka wa tarayyar Najeriya a fadan da take yi da ta’addanci.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha Maria Zakharova ce ta bayyana hakan, sannan kuma ta jinjinawa kokarin da gwamnatin ta Najeriya take yi a wannan fagen na kalubalantar masu wuce gona da iri.
Zakharova ta kuma ce, matsayar Rasha ba ta sauya ba akan yadda take kallon ta’addanci a matsayin barazana ga zaman lafiya na duniya.
Haka nan kuma ta ce, Rasha a shirye take ta bayar da taimako da kuma aiki tare da kungiyoyin kasa da kasa da cibiyoyin MDD da kuma tarayyar Afirka.
Dangane da Najeriya, Zakharova ta kara da cewa; Rasha a shirye take ta ci gaba da bai wa Najeriya taimako, kuma sojoji da jami’an tsaron kasar suna da kwarewa mai yawa da su ka samu a fagen fada da ta’addanci.”
Haka nan kuma ta yi ishara da yadda fararen hula da su ka hada mata da yara suke jin jiki matuka saboda ayyukan ta’addanci.
Kasar Najeriya dai tana fama da matsalolin tsaro daga kungiyoyin ta’addanci da su ka hada Bokoharam, Iswap da kuma barayin daji masu garkuwa da mutane.
A cikin kasa da mako daya an sace daliban makarantun arewacin kasar da dama, da hakan ya tilastawa mahukunta rufe makarantu a jihohi masu yawa.