Shugaban Afirka ta kudu, Cyril Ramaphosa ya soki kalaman takwaransa na Amurka Donald Trump na cewa ba zai gayyace shi taron kasashen gungun G20 mafiya karfin tattalin arziki na duniya a shekara mai zuwa a Florida.
Ramaphosa ya ce abin takaici ne yadda Trump ke ci gaba da daukar matakai bisa labaran da ba na gaskiya ba ko kuma aka yi musu kwaskwarima.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba zai gayyaci Afirka ta kudu taron na badi ba, da Amurka zata karbi bakunci, kuma ya nanata sukar da yake yi wa Afirka ta kudun, kan zargin cewa an aikata kisan kiyashi a Afirka ta Kudu a kan tsirarun fararen fata.
Amurka ta kauracewa taron na G20 na bana a Johannesburg, inda shugabanni suka amince da matakan da aka ayyana na magance matsalar dumamar yanayi da sauran matsaloli na duniya, duk da kin yardar Amurka.