Rahotannin leƙen asiri na Amurka ya bayyana cewa: Rarrabuwa kawuna na barazanar wargaza Isra’ila da kuma tayar da yakin basasa
Jaridar The Telegraph ta Burtaniya, a cikin wani rahoto da Henry Budken ya fitar, ya bayyana cewa: Haramtacciyar Kasar Isra’ila na fuskantar karuwar rarrabuwar kawuna a cikin gida wanda kan iya barazana wargaza hadin kan zamantakewa da kwanciyar hankali na siyasa. Waɗannan rarrabuwar kawuna sun samo asali ne daga takaddama mai zafi kan tilasta wa Yahudawan Orthodox shiga aikin soja, faɗaɗa matsugunan da ke Yammacin Kogin Jordan da kuma ƙaruwar matakan cin zarafi da ake yi wa Falasdinawa, wanda matsin tattalin arziki ya haifar sakamakon ƙaruwar kashe kuɗi a fannin soji.
Rahoton ya ambaci wani bincike na leƙen asiri na Amurka, wanda gwamnatin Amurka ba ta tabbatar da shi ba, yana mai gargadin cewa tarin waɗannan rikice-rikicen na iya fallasa Haramtacciyar kasar Isra’ila ga haɗarin da take fuskanta na yiwuwar wargajewar al’ummata har ma da barkewar yakin basasa.