Rahotanni : Isra’ila Ta Gaza Wajen Tunkarar Hare-hare Daga Yemen

Kafofin yada labaren Isra’ila sun rawaito cewa kasar ta gaza wajen tunkarar hare-haren makamai masu linzami da suke fitowa daga kasar Yemen. Kafar yada labaran

Kafofin yada labaren Isra’ila sun rawaito cewa kasar ta gaza wajen tunkarar hare-haren makamai masu linzami da suke fitowa daga kasar Yemen.

Kafar yada labaran Isra’ila ta “Maariv” ta jaddada gazawar gwamnatin kasar wajen tunkarar hare-haren da suke fitowa daga Yemen.

Jaridar ta bayyana cewa an harba makamai masu linzami sama da 200 da jirage marasa matuka 170 daga kasar Yemen zuwa yankunan da Isra’ila ta mamaye.

“Avi Ashkenazi” mai sharhi kan harkokin soji a gwamnatin Isra’ila a wata hira da ya yi da jaridar Maariv ya ce: “A yau, fiye da kowane lokaci, a bayyane yake cewa Isra’ila ba za ta iya tinkarar kasar Yemen ba.

Jaridar “Haaretz” ita kuwa ta rawaito harin da sojojin Yemen suka kai a safiyar ranar Asabar da makami mai linzami samfarin “Palestine 2”, wanda ya jikkata ‘yan Isra’ila 20.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments