Kafafen watsa labarai na Amurka sun ruwaito cewa Janar Dan Caine, Shugaban Hafsoshin Sojojin Sama, ya gargadi Shugaba Donald Trump game da hadarin da ke tattare da kai hari kan Iran.
Bayanin ya Ambato cewa akwai yuwuwar daukar irin wannan matakin ya yi tsada sannan kuma ya zama na dogon lokaci.
Washington Post ta ruwaito a ranar Litinin cewa Caine ya nuna damuwa a Fadar White House da Pentagon game da karancin makamai da rashin samun goyon baya da kawaye, wanda zai iya sanya ma’aikatan Amurka cikin hadari.
Hakazalika, Jaridar Wall Street Journal ta nuna cewa jami’an Pentagon suna cikin fargaba game da asarar da Amurka da kawayenta zasuyi, da kuma nakaso ga tsarin tsaron sararin samaniyar Amurka idan suka kai hari kan Iran.
Kamfanin labarai na Axios ya kara da cewa Caine ya yi gargadi game da “kasancewar Amurka cikin rikici mai tsawo.”
Amma Trump ya yi watsi da rahotannin a ranar Litinin, yana mai ikirari a shafinsa na Truth Social media cewa “ba daidai ba ne cewa Caine “ya adawa da shiga yaki da Iran.”
Shugaban na Amurka ya sake yin barazana ga Iran da al’ummarta cewa wata “mummunan rana” zata zo a gare su idan ba a cimma yarjejeniya ba a yayin tattaunawar nukiliya da ake ci gaba da yi domin maye gurbin yarjejeniyar nukiliya ta 2015, wacce Trump ya yi fatali da ita a lokacin wa’adin mulkinsa na farko.
A ranar Alhamis mai zuwa ake sa ran bangarorin zasuyi ganawa ta uku a Genava a yunkurin cimma wata sabuwar yarjejeniya.