Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da gwamnatin Isra’ila na a matakin karshe,” in ji wani jami’in Qatar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Qatar Majed Al-Ansari ya fada a wani taron manema labarai a ranar Talata cewa ana ci gaba da tattaunawar a shiga tsakanin AMurka,Qatar da kuma Masar.
Ya ce “Tattaunawar tana gudana ne kan bayanai na karshe amma mun kawar da manyan matsalolin.”