Gwamnatin kasar Qatar ta yi tir da fray ministan HKI Banyamin Natanyahu, kuma ta bukaci a gurfanar da shi a gaban kuliya, saboda hare-haren ta’addanci da kai birnin Doha babban birnin kasar a ranar Laraban da ta gabata .
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Firay ministan kasar Qatar yana fadar haka a yau Alhamis a birnin Doha ya kuma mkara da cewa, duk da cewa dama ana nemansa a kotun ICC saboda laifukan yaki, kasar Qatar tana bukatar a gaggauta kaishi gaban kuliya.
Hare-haren dai sun jawo tir da allawadai kan HKI a mafi yawan kasashen Duniya, da kuma manya-manyan kungiyoyi na kasa da kasa. Musamman ganin cewa kasar Qatar ce babbar mai tsiga tsakani don dawo da zaman lafiya a yankin da HKI take fafatawa da kungiyar Hamas a Gaza tun ranar 7 ga watann Octoban shekara ta 2023.
Firay ministan y ace samuwar wakilan kungiyar Hamas masu tattaunwa da dayan bangen a Doha sanenne ne ga HKI da kuma Amurka. Kasar Qatar bata tara jami’an kungiyar Hamas a Doha don basu mafaka na din din ba.
Dangane da wannan an ji Natanyahu yana maida martani kan cewa kasar Qatar ta tara yan ta’adda a birnin Doha, don haka ta tara mikaya HKI don haka abinda ta yi dai-dai ne. Kuma ya sha alwashin bin yan kungiyar Hamas a duk inda suke don halakasu.