Qatar Na Ci Gaba Da Kokari Na Rage Sabanin Tsakin Iran Da Amurka

kasar Qatar ta bayyana shirinta na ci gaba da kokari na rage sabanin dake tsakanin kasashen iran da Amurka

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar Majed al-ansari ya bayyana cewa ana ci gaba da kokari wajen ganin an rage banbance banbance dake tsakanin Washington da kuma birnin Tehran inda dukkan bangarorin biyu suka yi musayar bukatu, kuma kasashen yankin suna yin aiki tare wajen ganin an samu mafitar diflomasiya

Da yake hira da gidan talabijin din Aljazeera a birnin doha kakakin ya bayyana cewa Washington da Tehran suna duba bukatun da suka aike wa juna a matsayin wani bangare na kokarin da ake yi na ganin an cimma matsaya kan bukatun kowanne bangare domin kulla yarjejeniya

Haka zalika ya kara da cewa kasar Qatar tana aiki sosai da sauran kawayenta da kuma hukumomi na kasa da kasa wajen ganin an kawo karshen rikicin, kuma dukkan shuwagabannin yankin suna ci gaba da tuntubar juna na ganin an cimma matsaya da kuma kaucewa sake fadawa cikin wani sabon rikici

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted