Qatar:  Hamas Ta Amince Da Sabuwar Yarjeniya Da HKI

Gwamnatin kasar Qatar a birnin Dubai ta bada sanarwan cewa kungiyar Hamas ta amince da wata yarjeniya wacce HKI ta amince a baya, don haka

Gwamnatin kasar Qatar a birnin Dubai ta bada sanarwan cewa kungiyar Hamas ta amince da wata yarjeniya wacce HKI ta amince a baya, don haka akwai fatan HKI zata sake amincewa da ita sannan a tsagaita budewa juna wuta nan gaba kadan.

Shafin yanar Gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Qatar  Majed Al-Ansari yana fadar haka ya kuma kara da cewa idan HKI ta amince da ita, ana iya tsagaita junawa Juna wuta. Ya ce mafi yawan abinda sabuwar yarjeniyar ta kunsa kusan babu bambanci da wacce HKI ta amince da ita a   baya.

Sai dai Al-sari ya bayyana cewa har yanzun HKI bata bada amsa kan yarjeniyar ba. Yace abu mai muhimmanci shi ne ya kasance dukkan mabgarorin biyu sun amince da abinda yarjeniyar ta kunsa, kuma yanzu abinda muke aiki a kansa ne.

Da aka tambaye shi bambancin wannan yarjeniyar da abinda Steve Witkoff a gabatar a baya, Ansari ya bayyana cewa baya son shiga cikin dallah dallan yarjeniyar saboda har yanzin basu da tabbacin HKI zata amince da ita ba.

Qasar Masar da kuma Qatar ne suke kaiwa sama da kasa don ganin an cimma tsagaita budewa juna wuta ko menene karanncinsa. Wanda zai bada dama a shiga da bukatin mutanen Gaza zuwa yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments