Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya ja kunnen Amurka dangane da yanda take mu’amala da JMI al-hali sun ganin yanda Amurkawa sun kasa hakuri kan tsadar man fetur wanda farashinsa ya tashi a kasar saboda rufa mshigar ruwa ta Hurmuz.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Qalibaf yana fadar haka a wani shafin yanar gizo, inda kuma ya sanya hotuna wadanda suke nuna yanda Amurkawa suke shan wahala kuma suke kokawa kan halin da shugaban ya jefasu sanadiyyar rufe mashigar ruwa ta Hurmuz.
Yace, duk tare da mamayar da kuma karfin da Amurka take da shi a duniya amma fili yake mutanen kasar sun tasirantu da tsadar farashin man fetur wanda rufe mashigar ruwa ta Hurmuz ya jawo. Y ace a fili yake Washington ba zata shake irin har wuya, ba tare da Tehran ta maida martani ba.
Qalibof ya gina maganarsa ne da rahoton Bankin J.P. Morgan ya bayar na cewa fitar da danyen man fetur a duniya ya fadi da ganga miliyon 555, sannan nan gaba Kaden idan wannan halin ya ci gaba duniya ba zata jurewa musibar ba.