Shugaban Majalisar Dokokin Iran ya mayar da martani ga sakataren harkokin wajen Amurka cewa: Da yardan Allah Amurka zata durƙusa a gaban Iraniyawa
A martanin da ya mayar ga ikirarin Marco Rubio, Shugaban Majalisar Dokokin Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya rubuta cewa: “Waɗanda ke neman yin koyi da gadon Alexander za su gamu da irin ƙaddarar da Valerian ta yi musu; za su durƙusa a gaban hamayyarsu!”
A cewar Kamfanin Dillancin Labaran Mehr na kasar Iran, Shugaban Majalisar Dokokin kasar Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya rubuta a shafinsa na sada zumunta, yana mai mayar da martani ga kalaman “marasa ma’ana” na baya-bayan nan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi game da wayewar Iran cewa: “A tsawon tarihi, al’ummar Iran sun fuskanci waɗanda suka naɗa kansu shugabannin duniya kuma suka nemi share tsoffin wayewar duniya daga kan doron kasa.”
Ya ƙara da cewa: “Makiya sun zo da karfin wuta, amma sun tafi cikin ƙura da kunya.”
Qalibaf ya jaddada cewa: “Waɗanda ke neman yin koyi da gadon Alexander za su fuskanci irin makomar Valerian; za a durƙusar da su.”