Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba yin sassauci game da tsibiranta guda uku ba
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da da’awa mara tushe da ke kunshe cikin sanarwar hadin gwiwa da ministocin harkokin wajen kungiyar hadin kan kasashen Larabawan yankin tekun Fasha (PGC) da kungiyar Tarayyar Turai suka yi, gami da maimaita da’awar banza da wofi dangane da tsibiran Iran guda uku.
Ya kara da cewa: Amincin kasar Iran da matsayinta suna tabbata ne da jinin dubban daruruwan matasan wannan al’ummar kasa, kuma al’ummar Iran ba za su taba lamunta duk wani hasashe na irin wannan rainin hankali ba.