Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin zai ziyarci kasar Sin a ranakun 16 da 17 ga watan Mayu bisa gayyatar Xi Jinping, kamar yadda fadar Kremlin ta sanar a yau Talata.
A yayin ziyarar tasa, shugaban na Rasha zai ziyarci birane biyu – Beijing da Harbin.
Wannan ita ce ziyarar farko ta Mista Putin zuwa kasashen waje tun bayan rantsar da shi a ranar 7 ga Mayu, 2024.
A yayin ziyarar biyu za su tattaunawa kan batutuwan da suka shafi cikakken hadin gwiwa da mu’amala bisa manyan tsare-tsare.
Za su yi musayar ra’ayi kan batutuwan da suka fi daukar hankalin duniya da na shiyya-shiyya Shugabannin biyu za su halarci bikin cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen Rasha da Sin