Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yay aba da aikin kananan jiragen ruwa na kasar Iran wadanda ake kira ‘mosquito Fleet’ wadanda suke ayyukan masu muhimmanci a yakin da Iran take fafatawa da sojojin Amurka a kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labaran (ISNA) na kasar Iran ya nakalto shugaban kasar Rasha yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a taro da sojojin ruwa na kasar a cikin yan kwanakin da suka gabata.
Putin, yace : Ku kaloli abinda yake faruwa a yammacin Asia, inda kananan jiragen ruwa na kasar Iran suke ayyukan ban mamaki, kuma yakamata sojojin ruwa na kasar Rasha su yi amfani da irin wadannan kananan jiragen ruwan,
Dakarun IRGC da kuma sojojin ruwa na kasar Iran suna amfani da wadannan kananan jiragen ruwa ne, wadanda suka watsa su a ko ina a cikin tekun farisa, don lalata manya manyan jiragen ruwa masu tafiya a hankali, ko su lalata tankunan man fetur na makiya, tare da amfani da makamai masu linzani wadanda aka girka a cikinsu.
Sau da dama wadan nan taron kananan jiragen ruwa sun kori manya manyan jiragen ruwa daga yankin yammacin Asiya a yakin da Amurka da HKI suka dorawa JMI.