Putin Ya Ja Kunnen Nato Kan Kai Hari Kan Kaliningrad

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ja kunnen kungiyar tsaro ta NATO kan kai hari a garin Kaliningrad wanda yake kan iyakar kasar da Poland

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ja kunnen kungiyar tsaro ta NATO kan kai hari a garin Kaliningrad wanda yake kan iyakar kasar da Poland da kuma Lithuania.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa kasar Rasha zata yi amfani da dukkan makaman da take da su daga cikin har da makaman kare dangi don maida martani ga kasashen Turai da kuma NATO.

A cikin yan kwanakin da suka gabata kasashen Turai karkashin laiman kungiyar tsaro ta NaTO suna gudanar da atisayen soje a tekun Baltic, wanda bai da nisa da kasar Rasha, kuma mai yuwa su fadawa kasar Rasha ta yaki, inda kuma zasu fadada yakin na Ukraine zuwa kasashen Turai.

Putin ya kara da cewa “Idan sun kaiwa Rasha hare hare daga cikin har da Kaliningrad tarayyar Rasha tana iya amfani da dukkan makaman da take da su daga ciki har da makaman nukliya don kare kanta”

Shugaba Putin Rasha bata da wani shiri na kaiwa kasashen Turai hare hare, amma idan sun kai hari kan kasar Rasha zasu halatta mata amfani da dukkan makaman da take da su don kare kanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted