Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ba da shawarar yin tattaunawa “kai tsaye” ba tare da sharadi ba” tsakanin kasarsa da Ukraine a ranar 15 ga Mayu a Istanbul.
A martanin da ya mayar, shugaban na Ukraine ya ce a shirye ya ke don tattaunawa kai tsaye, amma ya zama dole a tsagaita bude wuta a gabanin haka, yana mai nuni da shawarar da kawayensa na yammacin duniya suka bayar na tsagaita bude wuta na kwanaki 30 ba tare da sharadi ba daga ranar Litinin.
Ba tare da yin tsokaci a kai tsaye kan shawarar kasahen ba, shugaban na Rasha ya caccaki turawan da ya ce sun yi wa Rasha “rashin ladabi da kakkausan lafazi” ya kuma ce ya kamata kafa sulhu ya zama wani bangare na tattaunawa kai tsaye kan rikicin da aka shafe sama da shekaru uku ana yi.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Recep Tayyip Erdogan ya yi maraba da shawarar Vladimir Putin na tattaunawa tsakanin Moscow da Kyiv a Istanbul, in ji fadar shugaban kasar Turkiyya.
“A yayin tattaunawar, shugaba Erdogan ya shaidawa shugaba Putin na Rasha cewa, a shirye Turkiyya ta ke ta karbi bakuncin tattaunawar da za ta kai ga cimma matsaya mai dorewa.”