Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa dakatar da budewa juna wuta a yakin Ukraine a halin yanzu yana hannun kasashen yamma da kuma ita Ukraine.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban Putin yana fadar haka a jiya Jumma’a a jawabin karshen shekara da ya gabatar a birnin Mosco. Ya kuma kara da cewa, Ba Rash ace ta fara wannan yakin ba. Yace an fara wannan yakin ne a juyin mulkin da aka yi a kasar Ukraine a shekara ta 2014. Kuma bayan haka an yi tsammaninc cewa za’a warware matsalolin da suka taso bayana juyin mulkin a tarin Minsk amma hakan bai tabbata ba. Wannan halin ya ci gaba har zuwa lokacinda Rasha ta ga cewa babau wata hanya da ta rage an banda yaki.
Putin ya ce ba’a kawo karshen yakin Ukraine ba sai tare da warware asalin matsalat da ta jawo yakin. Duk wata yarjeniyar tsagaita wuta wanda bait abo wannan ba, to yaki bai kare ba.
Daga karshe shugaban Putin ya bayyana cewa kasar Rasha tana son kawo karshen wannan yakin kuma bata son yaki a shekara ta 2026 mai zuwa. Amma sai dai mabudin wannan zaman lafiya na hannin kasashen yamma da kuma kasar Ukraine.
Dangane da tattalin arziki kasar Rasha bayan an kawo karshen yaki kuma, Putin ya bayyana cewa, idan an kawo karshen yaki kasashen Rasha da Turai suka hada kai ta GDP dinsu gaba daya idan a tara zai fi na kasar Amurka.
Wanda zai bawa kasashen Turai da Rasha kawo karshen dogaroda Amurka a kan al-amura da dama. Kuma zasu warware matsalolin tattalin arzikin da ke addabar Turai da Rasha a lokaci guda.
Sannan yace idan hakan bai faru ba, yana jin tsaron cewa tarayyar Turai zata bace gaba daya, a fagen tattalin arziki a duniya.