Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya karbi bakuncin shugabannin kasashen Afirka da su ka hada na Zimbabwe da na Burkina Fasa, inda su ka tattaunawa hanyoyin karfafa alaka a tsakanin kasashen nasu.
Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa da na Burkina Faso Ibrahim Taraore sun isa birnin Moscow domin halartar bikin cika shekaru 80 da samun nasara akan ‘yan Nazi na Jamus a lokacin yakin duniya na 2.
Bugu da kari shugaban kasar ta Rasha ya kuma gana da shugaban gwamnatin kwarya-karyar Falasdinawa Mahmmud Abbas Abu Mazin,inda su ka yi musayar ra’ayi akan yadda za a kawo karshen kisan kiyashin da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu.