Putin : Rasha Na Ba Da Gudummawa Ga Ci Gaban Nahiyar Afrika

Shugaban Rasha ya tabbatar da cewa Moscow na son raba fasahohi na musamman ga kasashen Afirka.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Poutine ya bayyana irin gudummawar da kamfanonin kasarsa ke ba da wa a fannin ci gaban nahiyar AFrika.

Mista Putin, ya bayyana hakan ne a wani bangare na jawabinsa na bude taron Afrika da Rasha kari na uku a birnin Moscow.

Shugaban na Rasha ya kuma tabbatar da cewa Moscow tana son raba fasahohi na musamman ga kasashen Afirka wadanda za su iya habaka kula da albarkatun ruwa. 

Ya kuma nuna cewa Rasha nai taimakawa wajen aiwatar da ayyukan makamashi sama da 30 a kasashen Afirka 16.

A hannun daya kuma ya ce Hukumar makamashi ta Rasha RusHydro a shirye take ta taimaka wa kasashen Afirka wajen tsara sabbin tashoshin wutar lantarki da kuma sabunta kayayyakin da ake da su.

Shugaban na Rasha ya kuma kara da cewa kasarsa na shiga cikin kokarin inganta yanayin tattalin arzikin kasashen Afirka da kuma rage musu nauyin basussukan da ke kansu.

 Ya bayyana cewa Rasha ta kafa shirye-shiryen hadin gwiwa da wasu kasashen Afirka don amfani da kudaden rage basussukan don daukar nauyin ayyukan kasa da suka mayar da hankali kan ci gaban tattalin arziki.

Jimillar, kasashe 48 ne daga cikin 54 na Afirka suka tabbatar da halartar taron.

Ana sa ran taron zai mayar da hankali kan noma, makamashi, zuba jari, kayayyakin more rayuwa, da fasaha.

Moscow dai na da niyyar, inganta hadin gwiwarta da Afrika bisa girmama juna da kuma samun damar samun albarkatu, abinci, takin zamani, da fasahohin zamani ga kasashen nahiyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted