Putin : Gabas ta tsakiya na daf da “fadawa yaki gaba daya”,

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya bayyana cewa yankin Gabas ta tsakiya na “daf ​​da fadawa yaki baki daya,” Yayin da ake ci gaba da

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya bayyana cewa yankin Gabas ta tsakiya na “daf ​​da fadawa yaki baki daya,”

Yayin da ake ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula a yankin, “Yakin na yaduwa zuwa kasar Lebanon, kuma sauren kasashen yankin ma abin ya shafe su.

barazanar arangama tsakanin Isra’ila da Iran ma ta karu sosai, inji Putin, ya sanya Gabas ta Tsakiya gaba daya daf da fadawa yaki,” in ji shi a jawabin da ya yi a taron kasashen BRICS a Kazan.

Dama sanarwar bayan taron kolin shugabannin na BRICS da ya gudana ranar Laraba a birnin Kazan na kasar ta Rasha, ya nuna damuwa game da rikice rikicen da duniya ke fama dasu.

Sanarwar ta mayar da hankali kan rikice-rikicen da ake fama da su a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kasar Ukraine, inda shugabannin suka bayyana matukar damuwa game da tashe-tashen hankula a zirin Gaza tare da yin kira da a gaggauta tsagaita wuta da dakatar da duk wani tashin hankali. 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments