Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Iran, Massoud Pezeshkian sun tattauna kan halin da ake ciki a baya bayan nan a kasar Siriya.
Shugabannin biyu sun jaddada muhimmancin hada kai tare da shigar da kasar Turkiyya cikin tsarin tsarin Astana don warware halin da ake ciki a Siriya.
Ofishin shugaban kasar Rasha ya sanar da tuntubar shugabannin Rasha da Iran a cikin wata sanarwar manema labarai ta gaggawa.
Kamfanin dillancin labaran Sputnik ya rawaito daga wata sanarwa da fadar shugaban kasar Rasha ta fitar tana bayyana cewa : Putin da Pezeshkian sun tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban hadin gwiwa tsakanin Rasha da Iran a fannoni daban-daban.
Tunda farko dama shugaban kasar ta Iran, Masoud Pezeshkian ya ce Tehran a shirye take ta inganta hadin gwiwa da kasar Syria domin shawo kan rikicin da ke ci gaba da addabar kasar ta Larabawa, sakamakon sake bullar ta’addanci.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaba Bashar al-Assad na Syria a jiya litinin, Pezeshkian ya ce Iran na sa ido sosai kan abubuwan dake faruwa a Syria.
“Mun yi imanin cewa, Siriya za ta sake yin nasara kan makirce-makircen sahyoniyawan, kuma muna kara jadadda goyan bayan mu ga gwamnati da al’ummar Siriya don cimma wannan manufa.”