Hukuma mai kula da mashigar ruwa ta Hurmuz na kasar Iran ta bayyana cewa ta kai hare hare kan jiragen dakon man fetur na Emirat guda uku a kwanakin da suka gabata ne saboda sabawa doka.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ta nakalto majiyar PGSA na fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa, dakarun IRGC Navy sun buge jiragen ruwa da dama a cikin yan kwanakin da suka gabata saboda kokarin sace hanyar wucewa ta Hurmuz, uku daga cikinsu mallakin Emirat ne, ko kuma wadanda ta yi hayarsu.
Labarin ya kara da cewa, wadansu daga cikin jiragen sun yi kokarin sace hanyar wucewa a cikin watanni da suka gabata ba tare da nasara ba. Ya kuma kara da cewa, jiragen sun hada da Al Ruwais, Sinbad da kuma Mersin Prosperity, duk sun yi kokarin sace hanyar wucewa da mashigar ba tare da samun nasara ba.
Daga karshen hukumar PGSA ta gargadi kamfanin da suke bada jiragen ruwa haya, ko kamfanonin Inshora ko kuma wadanda suke taiamakwa irin wadannan jirage, su yi hattara don suna iya rasa rayukan matuka ko ma’aikatan jiragen, ko su fuskanci hanasu wucewa nan gaba. Banda haka hukumar tana iya kwace jirgin ko ta tilasta masusu biyan tara mai yawa.