Shugaban Kasar Iran ya bayyana cewa: Bai kamata a bar kowa shi kaɗai ba wajen biyan buƙatun rayuwa na yau da kullun
Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya jaddada cewa: Ana ba da fifiko ga waɗanda suka fi buƙatarta a rayuwarsu ta yau da kullun kuma kada a bar kowa shi kaɗai wajen biyan buƙatunsu na asali.
A cewar kamfanindillaqncin labaran ISNA na kasar Iran, Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezhakian ya rubuta a shafinsa na sada zumunta na X cewa: “Albarkatun jama’a na ƙasar na kowa da kowa ne, amma a cikin mawuyacin hali da ake cikii na yau, adalci yana buƙatar a mai da hankali kan gwamnati musamman ga gidaje marasa galihu da marasa kuɗi. Ana ba da fifiko ga waɗanda suka fi buƙatarta a rayuwarsu ta yau da kullun. Bai kamata a bar kowa shi kaɗai wajen biyan buƙatunsa na asali ba.”