Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian zai fara wani rangadi a kasashen Tajikistan da Rasha, inda zai kai ga rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta dogon lokaci mai cike da tarihi da Moscow. Ziyarar ta jaddada kokarin da Tehran ke yi na zurfafa alaka da manyan kawayenta da kuma inganta hadin gwiwar tattalin arziki da siyasa a cikin sauyin yanayi na duniya.
A cewar babban darektan hulda da jama’a na ofishin shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian zai tashi a yau Laraba domin ziyarar kwanaki uku a kasashen Tajikistan da Rasha, domin karfafa huldar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma kulla wata cikakkiyar yarjejeniya da takwaransa na Rasha Vladimir Putin.
Habibullah Abbasi ya bayyana ziyarar da shugaban ya kai a Tajikistan da Rasha a matsayin wani sauyi na dangantaka tsakanin Tehran, Moscow da Dushanbe.
Dangane da ziyarar Pezeshkian a Tajikistan kuwa Abbasi ya ce zai gana daban da shugaban Tajik, kakakin majalisar dokoki da kuma firaminista a Dushanbe babban birnin kasar.