Shugaban Iran Ya Tafi Taron Kungiyar Shanghai Ta “SCO”

Shugaban Iran Mas’oud Pezeshkian zai halarci taron kolin SCO a Bishkek, inda zai gana da shugabannin kasashe da manyan jami’an kungiyar.

Shugaban kasar Iran a yau Litinin zai kama hanyar tafiya ziyarar aiki zuwa kasar Kyrgyzstan

Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian zai yi tafiya zuwa Bishkek, babban birnin Kyrgyzstan, a yau Litinin domin halartar taron kwanaki biyu na kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO).

Habibullah Abbasi, Darakta Janar na Hulda da Jama’a a Ofishin Shugaban Kasa, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran “IRNA” cewa: A yau Lahadi, Shugaba Pezeshkian zai yi tafiya zuwa birnin Bishkek don halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai {SCO}.

Abbasi ya kara da cewa a lokacin ziyarar tasa, baya ga gabatar da jawabi a yayin zaman taron, Shugaba Pezeshkian zai gudanar da tarurrukan hadin gwiwa da shugabanni da manyan jami’an kasashe mambobin kungiyar da abokan hulda. Shugaba Pezeshkyan zai kuma halarci bikin buɗe gasar wasannin Nomad ta duniya karo na 6 ta shekara ta 2026.

An shirya gudanar da taron shugabannin ƙasashe na ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai (SCO) karo na 26 a ranakun 31 ga Agusta da 1 ga watan Satumban shekara ta 2026, a Bishkek, fadar mulkin kasar Kyrgyzstan, wanda zai jagoranci ƙungiyar a zagaye na shekara ta 2026.

Taken wannan taron shine “Shekaru 25 na ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai: Tare don Zaman Lafiya, Ci Gaba, da Ci Gaba Mai Dorewa.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted