Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana fatan cewa za a kawo karshen zalunci, tashin hankali, yaki, da kisan kare dangi a sabuwar shekara.
A wani sako da ya aike a ranar Litinin, Pezeshkian ya mika gaisuwar Kirsimeti da sabuwar shekara ga shugabanni da al’ummar kasashen da ke murnar bukukuwan.
Ya bayyana fatan cewa za a samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya a shekarar 2025.
A wani sako na daban, Pezeshkian ya kuma taya shugabanni da al’ummar kasashen da ke murnar sabuwar shekara.