Pezeshkian : MDD, Ta Gaza Wajen Kashe Wutar Rikici A Gabas Ta Tsakiya

Shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian, ya zargi Majalisar Dinkin Duniya da gazawa wajen “kashe wutar rikici” a Gabas ta Tsakiya. Shugaban ya bayyana hakan ne

Shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian, ya zargi Majalisar Dinkin Duniya da gazawa wajen “kashe wutar rikici” a Gabas ta Tsakiya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a birnin Kazan na kasar Rasha, a lokacin da yake halartar taron koli na kasashen BRICS.

Massoud Pezeshkian ya MDD, ta gaza wajen “kashe wuta” a yankin Gabas ta Tsakiya, a daidai lokacin da sojojin Isra’ila ke yaki a Gaza da kungiyar Hamas ta Falasdinu da kuma kungiyar Hizbullah a Lebanon.

“Har yanzu wutar yaki tana ci gaba da ruruwa a Falasdinu a zirin Gaza da kuma garuruwan Lebanon,” inji Pezeshkian, inda ya kara da cewa kunkiyoyin kasa da kasa musamman MDD sun kasa wajen dakatar da rikicin, da yace ya zama jawabi Majalisar Dinkin Duniya ta yi abinda ya dace don kashe wutar”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments