Pezeshkian: Iran za ta dauki matakan da suka dace domin shawo kan takunkumi

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta gwammace ta fuskanci mayar da takunkumin da aka kakaba mata, maimakon ta mutunta bukatar Amurka

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta gwammace ta fuskanci mayar da takunkumin da aka kakaba mata, maimakon ta mutunta bukatar Amurka da ke neman Iran din ta mika dukkanin tataccen Uranium da take da shi.

Da yake zantawa da manema labarai kafin ya bar birnin New York zuwa birnin Tehran, Pezeshkian ya yi karin bayani kan kokarin diflomasiyya a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya hada da ganawa da shugabannin kasashen Faransa, da Finland, da Switzerland, da Norway, da Iraki, da Bolivia, da kuma majalisar kungiyar Tarayyar Turai.

Yayin da yake nuni da cewa an cimma yarjejeniya da bangarorin Turai, ya nuna rashin jituwar da cewa duka daga bangaren  Amurka ne.

“Mun cimma yarjejeniya da bangarori na Turai, amma ra’ayin Amurka ya bambanta, kuma abu ne na hankali kan cewa Iran ba zata mika wuya ga dukkanin abin da Amurka take bukata ba, wanda hakan ita kuma ya yi hannun riga da maslaharta.

A ranar Jumma’a, Amurka da kawayenta, wadanda ake kira da E3, suka ki amincewa da wani daftarin kuduri daga Rasha da China, wanda ya nemi jinkirta aiwatar da tsarin dawo da takunkumai kan Iran a karkashin yarjejeniyar nukiliya ta  JCPOA.

Pezeshkian ya kara da cewa Amurkawa “suna son mu ba su dukkan sinadarin uranium da aka tace, wanda ba za a amince da shi ta kowace hanya ba.”

Shugaban na Iran ya nanata cewa da alama Amurka za ta matsa kaimi don “fara mayar da martani” na takunkumin a cikin watanni mas zuwa, yana mai kara  jaddada cewa idan aka tilastawa Iran yin zabi, to za ta zabi abin da ya dace da maslaharta da al’ummarta, mai makon  biyan bukatar da ba ta dace ba, yana mai shan alwashin cewa “duk da haka, za mu magance dukkan matsalolinmu.”

Ya ba da tabbacin cewa, an dauki matakan da suka wajaba don wannan yanayin, yana mai nuni da kawancen Iran da kasashe makwabta, BRICS, da kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da kuma juriyar al’ummar Iran, za su taimaka wajen  shawo kan wannan lamarin.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted