Shugaban Kasar Iran ya tabbatar da cewa: Iran ta dauki matakin da ya dace game da mashigar tekun Hormuz
A cikin wani sako da ya aike domin bikin Ranar Ruwa ta Duniya, Shugaban Kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya jaddada cewa ga Iran, teku ba wai kawai wani bangare ne na ruwa ba, har ma da wani albarkar Allah, wani muhimmin bangare ne na tarihin kasar, asalinta da rayuwarta, kuma daya daga cikin muhimman kadarorinta, a yanzu da kuma nan gaba.
Shugaban ya bayyana cewa: Yanzu haka masana’antar teku da ta ruwa sune ginshikai masu muhimmanci na ci gaban tattalin arziki, ci gaban yanki, samar da ayyukan yi da kuma hadewar duniya baki daya.
Ya kara da cewa, “Tare da fadin gabar tekunta a arewa da kudu da kuma matsayinta na dabarun sufuri a muhimman hanyoyin sufuri na yankin, kasar Iran cibiya ce ta duniya don cinikin teku, tattalin arziki, da kuma hanyoyin zirga-zirga.”
Ya jaddada cewa: Tsaro da ci gaba ba za a iya raba su ba, domin tsaron teku, tashoshin jiragen ruwa, da hanyoyin jigilar kaya suna share fagen tafiyar kasuwanci da ayyukan tattalin arziki cikin sauki.
Yayin da ci gaban tattalin arziki ke taimakawa, wajen karfafa matsayin kasar da karfinta na kasa.
Ya tabbatar da cewa Jamhuriyar Musulunci, ta hanyar dogaro da ƙwarewar sojojin ruwanta da duk waɗanda ke aiki a fagen ruwa, tana bin diddigin tsaro da kwanciyar hankali a hanyoyin ruwan yankin, da kuma tabbatar da tsaron hanyoyin ruwa da cinikayyar teku.