Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana bayan zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro ga daukacin yankin, yana mai cewa makwabciyarta Iraki tana samun kwanciyar hankali da farfardowa bayan fatattakar ‘yan ta’addar Daesh.
Pezeshkian na magana ne bayan ganawarsa da firaministan Iraki Mohammed Shi’a al-Sudani a Tehran babban birnin kasar.
“Jamhuriyar Iraki kasa ce mai muhimmanci a yankinmu kuma tana a matsayin abokiyar kawancen Iran.
Mun ji dadin yadda dangantakarmu ke tafiya a matakin da ya dace, kuma girman hadin gwiwar da muke da shi yana kara fadada a bangarori daban-daban a kowace rana,” in ji shugaban na Iran.
A nasa bangaren, firaministan Irakin, Sudani, ya ce ziyarar tasa na gudana ne bisa tsarin fadada hadin gwiwa tsakanin kasashen.
A bara shugaba Pezeshkian ya ziyarci kasar Iraki, inda ya gana da hukumomi da masu ruwa da tsaki a kasar ta Iraki.