Pezeshkian : Gwamnati na ta kudiri anniyar yaki da matsin attalin arziki da rashawa

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar warware matsalolin da suke tasowa na matsin tattalin arziki, cin hanci da rashawa, da

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar warware matsalolin da suke tasowa na matsin tattalin arziki, cin hanci da rashawa, da rashin gudanar da harkokin kudi yadda ya kamata musamman a fannin kakkasa yadda ake kashe kudaden kasashen waje a kasar.

Pezeshkian ya jaddada amincewar gwamnati ga aiwatar da shirin cikin sauri.

“Muna da tabbacin cewa ta hanyar aiwatar da wannan shirin a cikin dan gajeren lokaci, za’a samu bunkasa musamman ga wadanda ke da karancin kudadin shiga,” in ji shi.

Ya bayyana hakan ne a yayin wani taron da ya shugabanni da wakilai daga manyan kungiyoyi da masu ruwa da tsaki a kasar

Masu halartar taron sun sake jaddada alkawarinsu na tabbatar da tsaron abinci, da fannin kayayyakin noma masu mahimmanci, da kuma tabbatar da samar da kayayyaki na yau da kullun ga ‘yan kasa.

Tattaunawa ta kuma tabo dabarun inganta hulda, da saka hannun jari tare a manyan ayyukan kasa a fannoni kamar masana’antu, noma, kiwon lafiya, da makamashi.

Shugaban ya ƙara jaddada ƙudurin gwamnati na haɓaka samar da kayan masarufi a cikin gida a fannin masana’antu da noma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted