Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce al’ummar Iran na bukatar hadin kai fiye da kowane lokaci, kuma dole ne su hada karfi da karfe su tsaya tsayin daka wajen yakar zaluncin gwamnatin Isra’ila.
Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar dokokin kasar yau Litinin, inda ya yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin Isra’ila ta yi kan Iran wanda ya yi sanadin shahadar wasu kwamandojin soja da masana kimiyya na Iran da kuma fararen hula da dama.
“Makiya ba za su iya kawar da mu ko kuma al’ummarmu daga ta hanyar kashe-kashe, da kisa ba,” in ji Pezeshkian, ya kara da cewa, “Ga duk wani jarumin da ya fadi, daruruwan karin za su tashi su dauki tuta kuma su yi adawa da zalunci, laifuffuka, da cin amana.
Shugaban ya yi kira da a hada kan kasa, yana mai jaddada cewa Iran ba ita ce ta takalo wannan yakin ba.
“A yau, fiye da kowane lokaci, muna bukatar hadin kai, wajibi ne dukkanin al’ummar Iran su hadu wuri guda, su tsaya tsayin daka wajen yakar wannan ta’addanci, kuma ko wane irin bambanci ko ra’ayi ko matsala da ake da su, dole ne a yi watsi da su a yanzu, inji shuganan kasar ta Iran.