Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Kai Hare-Hare Kan Cibiyoyin Leken Asirin Isra’ila

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci sun kai hare-hare har sau uku kan cibiyoyin leken asirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Ma’aikatar hulda da jama’a ta dakarun kare juyin juya halin musulunci ta Iran ta fitar da sanarwa inda ta bayyana harin da aka kai kan cibiyoyin leken asirin haramtacciyar kasar Isra’ila a mataki na uku […]
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Sojojin Isra’ila Sun Kashe Kananan Yara Masu Yawa A Iran

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kashe adadi mai yawa na yaran Iran a cikin ta’addancin da suke yi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe kananan yara masu yawa na Iran a cikin wannan ta’asa da take gudanarwa kan Jamhuriyar […]
An Zartar Da Hukuncin Kisa Kan Dan Leken Asirin Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Iran

Iran ta zartar da hukuncin kisa kan jami’an leken asirin Hukumar leken asirin yahudawan sahayoniyya “Mossad” a safiyar yau Litinin A wani gagarumin farmaki da aka kai kan cibiyar leken asirin yahudawan sahayoniyya a cikin kasar Iran, an kama wani mutum tare da yi masa shari’a bisa zargin hadin kai da hukumar leken asirin ‘yan […]
Jami’an Tsaron Kan Iyakar Iran Sun Harbo Jiragen Masara Matuka 44 Na Sojojin H.K.Isra’ila

Jami’an tsaron kan iyakokin Iran sun harbo jiragen saman yaki marasa matuki ciki guda 44 a cikin sa’o’i 48 da suka gabata Kwamandan rundunar tsaron kan iyakokin kasar Iran Birgediya Janar Ahmad Ali Goudarzi ya bayyana cewa: An harbo jiragen sama marasa matuka ciki guda 44 da kananan jiragen saman yakin gwamnatin ‘yan sahayoniyya tare […]
Amurka Ta Rufe Ofishin Jakadancinta Da Ke Tel-Aviv Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Gwamnatin Amurka ta rufe Ofishin Jakadancinta da ke haramtacciyar kasar Isra’ila Jakadan Amurka a haramtacciyar kasar Isra’ila Mike Huckabee ya sanar a yau Litinin cewa: Wani makami mai linzami na Iran ya fado kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Tel Aviv, wanda ya yi barna kadan amma ba a samu rauni a tsakanin […]
Iran majalisa ta amince da nadin Ali Madinizadeh a mukamin ministan harkokin tattalin arziki da kudi

Majalisar dokokin Iran ta amince da Ali Madinizadeh, wanda shugaba kasar Pezeshkian ya gabatar a mukamin ministan harkokin tattalin arziki da kudi na kasar. ‘Yan majalisar dokokin Iran sun amince da nadin masanin tattalin arziki mai shekaru 43 a mukamin da kuri’u 171, yayin da 67 suka ki amincewa da shi, sannan 8 daga cikin […]
Pezeshkian : Dole ne mu tsaya tsayin daka kan zaluncin gwamnatin Isra’ila

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce al’ummar Iran na bukatar hadin kai fiye da kowane lokaci, kuma dole ne su hada karfi da karfe su tsaya tsayin daka wajen yakar zaluncin gwamnatin Isra’ila. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar dokokin kasar yau Litinin, inda ya yi Allah wadai da hare-haren wuce […]
Iran ta sake kai wa Isra’ila sabin hare-hare da makamai masu linzami

Dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) sun kaddamar da wasu sabbin hare-hare na makamai masu linzami a kan gwamnatin yahudawan sahyoniya a cikin daren jiya Lahadi. An jiyo karar fashewar abubuwa masu karfi a yankunan da aka mamaye na Upper da Lower Galilee, Haifa, Afula da Nazaret. Jim kadan bayan hare-haren, Dakarun kare juyin […]
Sojojin Iran sun gargadi ‘yan Isra’ila a yankunan da aka mamaye su gaggauta ficewa

Sojojin kasar Iran sun yi gargadi ga Isra’ilawa mazauna yankunan da aka mamaye, su gaggauta ficewa a daidai lokacin da Iran ke shirin kaddamar da hare-hare a yankin. A cikin wani sako da aka watsa ta gidan talabijin, Kanar Reza Sayyad, kakakin cibiyar sadarwa ta sojojin kasar ta Iran, ya gargadi mazauna yankin da cewa […]
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi tir da harin Isra’ila kan gininta a Tehran

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi kakkausar suka kan harin da sojojin Isra’ila suka kai kan daya daga cikin gine-ginenta a Tehran babban birnin kasar, wanda ya yi sanadin jikkatar mutane da dama ciki har da ma’aikatan ma’aikatar. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Saeed Khatibzadeh, a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi, ya yi […]