Pezeshkian: Babu Batun Tattaunawa Da Amurka A Karkashin Matsin Lamba

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka ga matakin da gwamnatin Trump ya dauka kan Iran, yana mai bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi kakkausar suka ga matakin da gwamnatin Trump ya dauka kan Iran, yana mai bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba Ukraine ba ce, kuma ba za ta yi shawarwari da Amurka bisa barazana ko tilasci  ba.

“Dole ne mu kiyaye dangantaka da duniya. Ba ma son mu yi sabani ko jayayya da kowa, amma hakan ba yana nufin za mu durkusa cikin wulakanci a gaban kowa ba,” in ji Pezeshkian yayin wani taron kungiyar ‘yan kasuwan Iran a Tehran a ranar Talata.

“Muna iya mutuwa da daraja, amma ba za mu taɓa rayuwa cikin kunya da kaskanci ba.”

Pezeshkian ya yi watsi da abin da ya bayyana a matsayin wa’adi daga Donald Trump, yana mai nuni da wata wasika da aka ce shugaban Amurka ya aike zuwa Iran.

Wasikar ta bukaci Tehran da ta dakatar da shirye-shiryenta na nukiliya da makamai masu linzami da kuma daukar wasu matakai domin samun sassaucin takunkumi.

Ya soki Trump da rashin mutunta takwaransa na Ukraine, Volodymyr Zelensky, yayin da ya matsa masa lamba kan ya amince da wata yarjejeniya da Rasha.

Shugaban na Iran ya ce halin da Trump ya nuna a ganawarsa da  Zelensky a fadar White House abin kunya ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments