Shugaban kasar Iran Dr Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa ba wanda ya isa ya maida kasar Iran saniyar ware a dai dai lokacinda take makobtaka da kasashen 15.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya nakalto shugaban yana fadar haka kafin ya tashi zuwa kasar Turkamanistan inda zai halarci tarurruka har guda biyu, mna farko shi ne taron kasashen masu gamayya a don amfanin kansu ko CIS da kuma taron kasashe nab akin ruwan tekun Caspian.
Labarin ya kara da cewa, a taron shugaba Pezeshkiyan zai kulla dangantaka da tattalinb arziki siyasa tsaro da sauransu da wdan nan kasashe. Wadanda Amurka ba zata iya hanasu kulla wadannan hula da JMI ba. Don haka tare da wadan nan makobta takunkuman tattalin arzikin da Amurka ta dorawa JMI ba zai kai ko in ba.
Yace ziyara zuwa tarurruka a Turkamanistan zai bawa kasar Iran damar ganawa da shuwagabannin wannan yakin wanda ko wannensu yana fatan kulla dangantaka da kasar Iran ta ko wani iri ne.