Pezeshkian: An Shirya Samar Da Makamashi Ga Masana’antu

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewe: Masana’antu ya kamata su zama ɓangare na ƙarshe da za su fuskanci matsalolin makamashi Da yake magana game da

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewe: Masana’antu ya kamata su zama ɓangare na ƙarshe da za su fuskanci matsalolin makamashi

Da yake magana game da matsalolin rashin daidaiton makamashi da kuma barnar da hare-haren makiya suka yi wa kayayyakin iskar gas na Iran, Shugaban ya ce: “Sun fuskanci rashin daidaiton makamashi a baya, kuma yanzu, da harin da aka kai kan kayayyakin iskar gas na Iran, rashin daidaiton ya kara ta’azzara; saboda haka, ana sa ran za mu fuskanci matsaloli a lokacin hunturu.”

A cewar kamfanin dillancin labaran ISNA, Mas’oud Pezeshkian ya bayyana a taron shekara-shekara na kasuwar babban birnin Iran cewa: Kasar Iran tana cikin yakin da ba shi da daidaito kuma ba shi da adalci kuma ya fayyace: “Gaskiyar magana ita ce Iran tana cikin yaki; yaki mara daidaito kuma ba shi da adalci wanda gungun masu zaluntar mutane, azzalumai kuma masu wuce gona da iri suka yi niyyar kifar da gwamnatin kasar, amma mutane ba su yarda ba kuma jami’an tsaron kasar da na soji sun mayar da martani da karfi.”

Pezeshkian ya ci gaba da cewa: “Masu zuba hannun jari, masu samarwa, da masu fafutukar kasuwa suma sun sarrafa kasuwar ta yadda maƙiya suka ji takaici; Ra’ayin maƙiya shine za a yi yunwa a ƙasar, ba za a sami kayayyaki a kasuwa ba, kuma za a dakatar da zagayar samarwa. Duk da haka, a yau Iran ta ga cewa kayayyaki suna samuwa a kasuwa kuma har yanzu ana ci gaba da aikin samar da kayayyaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted