Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana aiki tsakanin Iran da kungiyar
‘Eurasian Economic Union’ ko ‘EAEU’ hanya ce mai kyau ta karfafa JMI da kuma sannan da kasashen kungiyar masu karfi.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a wani sakon da ya aika ga kungiyar ta (EAEU) a ranar Asabar wanda kuma jakadan kasar Iran a Rasha Kazem Jalali ya karanta shi a wani taron kungiyar da aka gudanar a birnin St. Petersburg na kasar Rasha.
Labarin ya kara da cewa taron wanda ya sami halattar shuwagabannin kasashen Rasha, Belarud,Kazakhstan, Kyrgyzstan da kuma firai ministan kasar Armenia ya nuna irin ci gaban da ake samu a cikin kungiyar da kuma hadin kai da aiki tare da kasashen kungiyar suke da shi.
Shugaba Pezeshkian, a cikin sakon nasa ya kara jaddada cewa gwamnatinsa tana aiki don ganin an sami hadin kan kasashen kungiyar bisa al-adu da kuma tarihin da suka hada kasashen kungiyar.
Shugaban ya kammala da cewa, kasar Iran tana cikin wasu kungiyoyi musu muhimmanci a yankin da kuma Duniya, kamar su BRICS, shangghai da kuma ECO amma duk da haka tana bada matukar muhimmanci ga kungiyar EAEU a tsarinta na harkokin waje. Daga karshe yace, a halin yanzu hulda tsakanin Iran da kasashen kungiyar EAEU yana cikin yanayinda yakamata ya fi haka.