Hadin gwiwar Iran da Eurasia ya share fagen samar da yanki mai karfi (Pezeshkian)

Shugaban kasar Iran Massoud Pezeshkian ya bayyana hadin gwiwa na tsakanin Iran da Kungiyar Tattalin Arzikin Eurasia (EAEU) a matsayin wata dabara ta dogon lokaci da nufin karfafa ikon mallakar kasa da kuma kafa cibiyar samar da wutar lantarki ta yankin.    A cikin wani sako da ya aike wa Majalisar Koli ta Kungiyar Pezeshkian, […]

Rasha na binciken kisan wani Janar din sojinta a harin bam a Moscow

A Rasha an fara gudanar da bincike kan kisan wani janar din sojin kasar a wani harin bam a kudancin Moscow. Kwamitin Binciken da aka kafa ya tabbatar da mutuwar janar din wanda shi ne shugaban sashen hora na ayyuka na rundunar sojojin Rasha sakamakon wani abu da aka sanya a karkashin motarsa ​​a gundumar […]

Tsaron Iran ba ya cikin abubuwan tattaunawa_Baghaei

Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa karfin tsaron kasar bay a cikin abubuwan tattaunawa a kai. Mai magana da yawun Ministan Harkokin Wajen kasar Esmaeil Baghaei ne ya bayyana hakan. M. Baghaei ya ce karfin tsaron Iran an tsara shi ne don dakila duk wani hari daga makiya kuma ba a shawarwari akan sa. […]

AFCON :  Morocco ta lallasa Comoros 2-0, Mali da Zambia sun tashi 1-1

A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na AFrika da yanzu haka ke gudana a Morocco,  kasar mai masaukin baki Morocco ta lallasa Comoros da 2-0 a wasan bude gasar a jiya. A ranar Litini Mali ta yi kunnen doki da Zambia 1-1 Afrika ta Kudu wqta karawa da Angola Sai kuma Masar […]

Amurka Ta Sake Kwace Jirgin Dakon Man Fetur Na Uku Na Kasar Venezuela

Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ya Ambato wasu jami’an kasar Amurka suna fada a jiya Lahadi cewa, sun kwace wani jirgin dakon man fetur na kasar Venezuela a gabar Ruwan wannan kasa, da shi ne na uku a cikin kasa da mako daya. Sai dai jami’an gwamnatin Amurka da su ka yi magana da kamfanin dillancin […]

An Daure Tsohon Ministan Tsaron Kasar Benin A Karkashin Binciken Yunkurin Juyin Mulki

Mahukunta a kasar Benin sun kama da daure tsohon ministan tsaro kasar   Candide  Azannai a karkashin binciken da ake yin a yunkurin juyin mulkin da bai kai ga yin nasara ba a farkon wannan watan na Disamba. Azannai dai shi ne shugaban jam’iyyar adawa, yana fuskantar tuhumar kitsawa gwamnati makarkashiya, da kuma yin tunzura domin ayi […]

An Kashe Wani Kwamandan Sojan Rasha A Birnin Moscow

A birnin Moscow na kasar Rasha an sanar da cewa an kashe wani babban kwamandan sojan kasar ta hanyar tashin bom a cikin motarsa a yau Litinin. Hukumar bincike ta tarayyar Rasha ta ce, janar din da aka kashe shi ne shugaban bangaren bayar da horo na Babbar cibiyar sojan kasar. Laftanar janar Fanil Sarvarov […]

Pezeshkian: Aiki Tare Da EAEU Mabudin Karfafa Kasashen Kungiyar Ne

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana aiki tsakanin Iran da kungiyar ‘Eurasian Economic Union’ ko ‘EAEU’ hanya ce mai kyau ta karfafa JMI da kuma sannan da kasashen kungiyar masu karfi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a wani sakon da ya aika ga kungiyar ta (EAEU) […]

Iran da Pakistan sun jaddada muhimmancin kara bunkasa harkokin kasuwanci

Mataimakin firai minista na kasar Pakistan da Ministan harkokin wajen kasar sun zanta ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi a cikin makonni biyu a jare inda suka tattauna kan dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma sauye-sauyen da ake sami a yankin Asia ta kudu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar […]

Burkina Faso, Mali Da Nijer Sun Kafa Runduna Ta Tsarin Yankin Sahel

A birnin Bamako na kasar Mali shugaba kasa Janar Assimi Goita ya jagoranci bikin kafa runduna ta yankin Sahel wanda ya hada kasashen uku wato Mali Borkina Faso da kuma Nijer. Wannan dai shi ne mataki na baya bayan nan wanda kasashen uku na Sahel suka dauka don tabbatar da karfinsu a yankin, da kuma […]

Amurka Tana Kokarin Kwace Wata Tankan Mai Ta Venezuela Na Uku

Gwamnatin shugaban kasar Amurka Donal Trump ta kara karfi wajen tabbatar da kofar ragon da ta shelanta kan kasar Venezuela inda a jiya Lahadi tana kokarin kwace tankar dakon mai na kasar ta Venezuela karu na uku. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa gwamnatin kasar Amurka tana son gurgunta kamfanin hakar […]

Ministan Harkokin Wajen HKI Ya Bukaci Yahudawan Australia Su Dawo HKI Da Zama

Ministan harkokin waje na HKI Gideon Saar ya bukaci yahudawan kasar Autralia sun dawo HKI bayan hare-haren da aka kai masu a makon da ya gabata a birnin Sydney cibiyar kasuwancin kasar wanda ya kaiga kashe yahudawa da dama. Jaridar ARABNEWS ta kasar Saudia ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Lahadi, ya kuma […]